Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mai tsaron lafiyar Janar din sojojin Iran

‘Yan bindiga sun kashe mai tsaron lafiyar wani Janar na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran yau Asabar, a wani hari da suka kai kan wani shingen binciken ababan hawa a yankin kudu maso gabashin kasar ta Iran.

Tutar kasar Iran.
Tutar kasar Iran. AFP - STRINGER
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Iran ya ce, an kai harin ne a Sistan-Baluchistan, lardin da ke kan iyaka da Pakistan da Afganistan, wanda aka saba kai hare-hare ko kuma fada tsakanin jami'an tsaro da kungiyoyi masu dauke da makamai a cikinsa.

An bayyana mai tsaron lafiyar da aka kashe Mahmoud Absalan, dan Janar Parviz Absalan, kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci a yankin.

Tuni dai jami’an tsaron Iran suka samu nasarar cafke wadanda suka kai harin.

Lardin Sistan-Baluchistan da ke fama da talauci, ya dade da zama wata matattarar arangama da kungiyoyin masu fasa kwauri, da kuma masu neman ballewa daga Iran ‘yan tsirarun kabilar Baluchi da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.