Isa ga babban shafi
Isra'ila - Hamaz

Mayakan Hamas sun kashe mutun daya da jikkata uku a birnin Kudus

Jami'an Isra'ila sun ce wani mayakan kungiyar Hamas mai kishin Islama ya bude wuta a birnin Kudus, inda ya kashe mutum daya tare da raunata uku, kafin daga bisani a harbe shi har lahira.

Mayakan Hamas dake fafatawa da dakurun Isra'ila.
Mayakan Hamas dake fafatawa da dakurun Isra'ila. MAHMUD HAMS AFP
Talla

Firanminista Isra’ila Naftali Bennett ya ba da umarnin karfafa tsaro tare da yin kira ga mutane da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana saboda barazanar kara kai hare-hare.

Wadanda suka jikkata da suka hada da farar hula biyu da ‘yan sanda biyu, an garzaya da su asibitin Hadassah na Kudus. Daya daga cikinsu, mai shekaru 30, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu, kamar yadda majiyoyin lafiya suka ce ba tare da karin bayani ba.

A cikin wata sanarwa da Bennett ya fitar ta ce "Da safiyar yau an kai wani mummunan hari a tsohon birnin Kudus." "A halin yanzu muna da mutum daya da ya mutu, uku kuma suka jikkata.

Tsohon birnin dai na cikin yankin gabashin birnin Kudus da Isra'ila ta mamaye, wanda Falasdinawa ke ikirarin cewa shi ne babban birnin kasarsu.

Isra'ila dai ta kwace gabashin birnin Kudus ne a yakin kwanaki shida a shekarar 1967, daga bisani kuma ta mamaye shi, a wani mataki da akasarin kasashen duniya ba su amince da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.