Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Za mu cimma matsaya da gwamnati amma kan wani sharadi-Taliban

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa, a shirye take ta shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin kasar, bisa sharadin sakar mata mayakanta dubu 7 da gwamnati ta kama.

Wasu daga cikin mayakan Taliban a Afghanistan
Wasu daga cikin mayakan Taliban a Afghanistan AP - Rahmat Gul
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin  da mayakan ke ci gaba da kai munanan hare-hare da kuma karbe iko da wasu yankunan kasar daga ikon gwamnati.

Mayakan Taliban sun ci gaba da matsa kai hare-haren ne tun bayan da dakarun Kungiyar Tsaro ta NATO da kuma dakarun kasar Amurka suka fara ficewa daga kasar, inda ake sa ran ficewarsu baki daya ranar 31 ga watan Agusta.

Ko a ranar Laraba, sai dai mayakan suka yi ikirarin kwace babbar hanyar da ke sada kasashen Afghanistan da Pakistan, abin da mahukuntan kasar suka musanta.

Rikicin Taliban ya sanya mutanen yankin kan iyaka tserewa zuwa Pakistan, inda lamarin  ya yi kamarin da sai da jami’an tsaro suka fara harba musu hayaki mai sa hawaye.

Tuni jami’an tsaron kan iyakar na Pakistan suka rufe iyakar kasar da Afghanistan don tantance masu turuwar shiga don tsira da rayukansu.

Ya zuwa yanzu, sama da mutane  dubu 1 da 500 ne suka tsere zuwa Pakistan daga Afghanistan a a ranar Laraba kadai, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.