Isa ga babban shafi

Hare-haren ƴan daba a Haiti sun tilastawa mutane dubu 53 barin matsugunansu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da dubu 50 ne suka tsere daga matsugunansu a birnin Port-au-Prince fadar gwamnatin Haiti cikin makwanni 3 da suka gabata don gujewa hare-haren da ƙungiyoyin ‘yan daba ke ci gaba da kaiwa babban birnin.

Hare-haren ƴan daba na ci gaba da tsananta a Haiti.
Hare-haren ƴan daba na ci gaba da tsananta a Haiti. © Odelyn Joseph / AP
Talla

Wani rahoto da hukumar kula da kaurar baƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ta bayyana cewa tsakanin ranar 8 ga watan Maris zuwa 27 mutane dubu 53 da 125 suk bar birnin Port-au-Prince, ƙari a kan mutane dubu dari da 16 da suka riga suka ɗaiɗaita a cikin ‘yan watannin nan.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka tsere a watan Maris sun doshi yankin kudancin ƙasar ne sakamakon rashin tsaro da rikicin da ake yi a yankunansu. 

Tun a ƙarshen watan Fabrairu ne gamayyar ƙungiyoyin ‘yan daba a Haiti suka dunkule waje guda inda suka rika farmakar ofisoshin ‘yan sanda da gidajen yari da filin tashi da saukar jiragen sama da kuma tashar jirgin ruwa a wani yunkuri da suke na ganin sun kawar da Firaministan Ariel Henry.

Rikicin ya haddasa matsananciyar matsalar jinkai, inda ƙarancin abinci ya kunno kai, kana aka samu wargajewar cibiyoyin lafiya da ababen more rayuwa a ƙasar.

A wani rahoto na dabam a makon da ya  gabata, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a cikin watanni ukun farkon wannan shekarar ta 2024, mutane dubu 1 da dari 5 da 54  ne aka kashe a rikicin na Haiti yayinda wasu dari 8 da 26 suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.