Isa ga babban shafi

Yawan mutanen duniya zai ragu sosai

Wani bincike ya nuna cewa, yawan al’ummomin kasashe daban-daban na duniya zai ci gaba da raguwa har zuwa karshen wannan karni.

Binciken ya nuna cewa, za a ci gaba da haihuwar jarirai masu yawa a kasashen Afrika.
Binciken ya nuna cewa, za a ci gaba da haihuwar jarirai masu yawa a kasashen Afrika. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Binciken ya kuma yi gargadin cewa, za a samu karuwar jariran da ake haihuwarsu a kasashen duniya masu tasowa, sabanin kasashen da suka ci gaba, inda haihuwar jariran za ta samu koma-baya, lamarin da zai haddasa gagarumin sauyi a tsakanin al’ummomin bangarorin biyu.

Tuni dai yawan haihuwa ya ragu kwarai da gaske a rabin kasashen duniya ta yadda ba za a iya habbaka adadin mutanen ba zuwa mizanin da ake bukata kamar yadda tawagar daruruwan masu binciken kasa da kasa ta bayyana a Mujallar The Lancet.

Kwararrun sun yi kokarin hasashen adadin yawan al’ummar duniya baki daya, inda suke amfani da tarin alkalumar haife-haife da mace-mace da kuma abubuwan da ke haddasa karuwar jama’a.

Nan da shekara ta 2050, za a samu raguwar kashi 1 bisa uku na yawan jama’ar kusan daukacin kasashen duniya  kamar yadda cibiyar da ta gudanar da binciken ta bayyana.

Binciken ya ayyana Samoa da Somalia da Tonga da Nijar da Chadi da Tajikistan a matsayin kasashen da ake sa ran za su samu karuwar al’umma fiye da mizanin da ake bukata nan da shekara ta 2100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.