Isa ga babban shafi

A karon farko Amurka ta fitar da kudirin dakatar da yakin Gaza

A karon farko Amurka ta fitar da wani kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ke kira kan gaggauta tsagaita musayar wuta a yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a daidai lokacin da ake ci gaba da gargadi kan tsanantar yunwa a Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken REUTERS - AGUSTIN MARCARIAN
Talla

A can baya, Amurka ta yi watsi da kudirin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, amma a yanzu Sakataren Harkokin Wajen kasar, Anthony Blinken ya tabbatar da sauya matsayar kasar. 

Blinken wanda ke ganawa da Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa biyar a wannan Alhamis a Masar, ya jaddada bukatar cimma yarjejeniyar gaggawa wadda ya ce za a alakanta ta da sakin Yahudawan da mayakan Hamas ke garkuwa da su tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Wannan na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza, inda Ma'aikatar Lafiyar Yankin ke cewa, akalla mutane 70 sun mutu a cikin daren da ya gabata sakamakon sabon farmakin na Isra'ila, kuma adadin mutanen da suka mutu a Gaza ya  kai dubu 32 a cewar hukumomin lafiyar.

Wani mazaunin Gaza mai suna Mahmud Abu Arar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa,

Muna cikin barci cikin aminci, sai mu ka ji karar fashewa. Fashewar ta yi kama da girgizar kasa.

 

Babban asibitin Gaza ya zama babbar tungar yaki bayan Isra'ila ta yi zargin cewa, mayakan Hamas na fakewa a cikin asibitin suna kaddamar da farmaki.

A yau Alhamis, hukumomin Isra'ila sun ce sun kashe mayakan Hamas sama da 140, yayin da Hamas din ke cewa, harin da ake kaddamarwa kan asibitin Al-Shifa, laifukan yaki ne.

Bayanai na cewa, akwai dimbin marasa lafiya da masu neman mafaka da ke samun matsuguni a cikin babban asibitin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.