Isa ga babban shafi

'Yan Finland sun fi kowa farin ciki da walwala a duniya

Wani rahoton kasashe mafiya farin ciki da Majalisar Dinkin Duniya ke fitarwa kowacce shekara, ya bayyana Finland a matsayin kasar da al’ummarta ta fi kowacce farin ciki a duniya shekaru 7 a jere.

Wasu mutanen Finland da ke shakatawa a birnin Helsinki
Wasu mutanen Finland da ke shakatawa a birnin Helsinki AP - Jussi Nukari
Talla

Cikin kasashe 10 mafiya farin ciki da ke kunshe a rahoton na Majalisar Dinkin Duniya, kasashen Denmark da Iceland da kuma Sweden ke biye da Finland wadda ta ci gaba da kasancewa kasa mafi farin ciki shekaru 7 a jere.

A bangare guda, Afghanistan ta ci gaba da kasancewa mafi karancin farin ciki a duniya, inda take matsayin ta 143 a jerin kasashen da al’ummominsu ke samun walwala, matsayin da take kai tun daga shekarar 2020 bayan da Taliban ta karbi ragamar mulkin kasar ta nahiyar Asiya.

Kazalika wannan ne karon farko da Amurka ke rikitowa daga matakin ‘yan gaba-gaba a sahun kasashe rukunin ‘yan 20 mafiya farin cikin, inda a wannan karon ta koma matsayin ta 23 biye da Jamus a matsayin ta 24, lamarin da ke nuna koma baya a yanayin farin cikin al’ummarsu.

Kasashen Costa Rica da Kuwait sun matsa gaba matsayin mafiya farin ciki daga rukunin ‘yan 20 a bara zuwa matsayin na 12 da 13.

Rahoton na bana bai kunshi ko da guda cikin manyan kasashe a sahun ‘yan 10n farko mafiya farin ciki ba, inda rahoton ke cewa yanayin farin ciki da walwala a kasashen Lebanon da Jordan da kasashen Gabashin Turai irinsu Serbia da Bulgari da kuma Latvia sun samu koma-baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.