Isa ga babban shafi
Zaben Amurka

Biden da Trump na takarar neman tikitin fafatawa a zaben shugaban kasa

Shugaban Amurka Joe Biden tare da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun shirya tsaf domin lashe tikitin tsaya wa jam’iyyunsu takara a wani gagarumin zaben fidda gwani da ke gudana a wannan Talatar, abin da zai ba su damar sake kafa tarihin fafatawa da juna a babban zaben kasar na watan Nuwamba mai zuwa.

Trump da Biden na takarar neman tikitin tsayawa takara a babban zaben watan Nuwamba.
Trump da Biden na takarar neman tikitin tsayawa takara a babban zaben watan Nuwamba. AFP - SERGIO FLORES,BRENDAN SMIALOWSKI
Talla

Ana gudanar da zaben na fidda gwani ne na wannan rana da ake yi wa lakabi da Super Tuesday a jihohin Amurka 16 da suka hada da wani yanki da ya taso tun daga Alaska da California zuwa Vermont da Virginia, yayin da daruruwan wakilan jam’iyyun ke cikin tsaka mai wuya.

Wannan zaben na fidda gwani shi ne mafi girma da manyan jam’iyyun Democrat da Republican ke gudanarwa a rana guda a kasar ta Amurka.

Duk da cewa, hankula sun fi karkata kan zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa, amma har ila yau, ana kada kuri’ar zaben wadanda za su tsaya takarar cike gurbi a majalisa a jihar California.

Kazalika ana zaben gwamna a jihar North Carolina, zaben da ke zama zakaran gwajin dafi ga jam’iyyar Democrat mai mulki gabanin babban zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.

Ana ganin cikin sauki Biden da Trump za su doke mutanen da ke fafatawa da su wajen neman lashe tikitin tsayawa takarar, yayin da wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, da dama daga cikin Amurkawa na ganin babu wanda ya cancanci sake jagorantar  kasar a tsakaninsu saboda rashin cikakkiyar lafiyar kwakwaluwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.