KWALON KAFA
Middlesbrough ta yi wa Chelsea ci 1-0 a gasar cin kofin Carabao
Wallafawa ranar:
Talla
Chelsea ta barar da da maki mai yawa, a yayin da Middlesbrough zakarar gasar Championship ta samu ‘yar takaitaciyar nasarar farko a kanta da 1-0 a gasar cin kofin Carabao da suka buga a filin wasa Riverside. Hayden Hackney ne, ya zura kwallon daya tilo, a zagayen farko na gasar.
Cole Palmer, ya rasa damarmaki uku masu muhimmanci, a yayin da Chelsea, ta buga kwallaye 18, inda ta barar da guda biyar a karo na shida a wannan kaka ta bana
Kocin Chelsea Mauricio Pochettino, ya sanar da cewa, mawuyacin abu ne a iya tantance namijin kokarin da suka bayar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu