Isa ga babban shafi

Saudi Arabia ta soki irin ruwan wutar da Isra'ila ke yi a yankin Gaza

Afirka – Yariman Saudi Arabia Muhammad bin Salman ya soki sojojin kasar Isra’ila dake kai munanan hare hare a Gaza, kwana guda kafin tarurrukan da ya kira wanda zasu mayar da hankali a kan tashin hankalin dake gudana a yankunan Falasdinawa.

Yarima Mohammed bin Salman tare da shugaban Amurka Joe Biden
Yarima Mohammed bin Salman tare da shugaban Amurka Joe Biden VIA REUTERS - BANDAR ALGALOUD
Talla

Salman ya shaidawa taron Saudiya da shugabannin Afirka cewar suna Allah wadai da hare haren da sojojin suke kaiwa a Gaza, wadanda ke ritsawa da fararen hula da kuma ci gaba da take hakkin Bil Adama wajen mamaye yankunan su.

Yayin da a karon farko yake tsokaci a bayyane dangane da yakin, Yariman ya bayyana bukatar dakatar da yakin wanda ke ci gaba da tilastawa mutane barin gidajen su da kuma haifar da matsalolin da zasu hana zaman lafiya a yankin.

A nashi jawabi, shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka ta AU, Moussa Faki Mahamat shima yayi Allah wadai da tashin hankalin dake matukar illa a kan Falasdinawa.

Mahamat yace suna bukatar daukar matakai na zahiri da zasu dakatar da lalata yankin Gaza da kuma kashe dubban mutane, domin bada damar samo hanyar siyasar da za’a samar da kasashe biyu a yankin.

Yarima Salman ya shaidawa shugabannin Afirkan cewar, Saudiya zata zuba jarin kudin da ya kai dala biliyan 25 a Afirka nan da shekarar 2030, abinda ya kusa ribanya adadin wadda ta yi a shekaru 10 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.