Isa ga babban shafi

Isra'ila za ta kori dubban 'yan Eritriya bayan zanga-zanga a Tel Aviv

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa kasar na tunanin korar ‘yan kasar Eritriya kimanin 1,000 da suka shiga zanga-zangar da ta koma tarzoma, abin da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama a Tel Aviv, ciki har da ‘yan sandan Isra’ila. 

'Yar Eritiriya sun yi arangama da jami'an Isra'ila a Tel-Aviv, ranar 2 ga Satumba, 2023.
'Yar Eritiriya sun yi arangama da jami'an Isra'ila a Tel-Aviv, ranar 2 ga Satumba, 2023. AP - Ohad Zwigenberg
Talla

 

A ranar Asabar ne, rikici ya barke lokacin da zanga-zangar adawa da wani taron gwamnatin Eritrea ya rikide zuwa tashin hankali, wanda ya raunata kusan mutane 140, ciki har da wasu masu neman mafaka 'yan Eritrea goma sha biyu da 'yan sandan Isra'ila suka harba. 

Rikicin dai ya fara ne lokacin da daruruwan 'yan Eritrea masu adawa da gwamnati suka yi yunkurin hana gudanar da taron a Tel Aviv, cibiyar kasuwancin Isra'ila. 

'Yan sandan Isra'ila sun ayyana taron a matsayin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba, inda suka yi umarnin kowa ya waste, abin da ya kai ga amfani da karfi. 

Sai dai masu zanga-zangar sun yi arangama da ‘yan sanda wadanda suka ce jami’an su 49 sun jikkata. 

Yayin da 'yan sanda da masu zanga-zangar Eritriya suka yi arangama a filin taron, a bangare daya kuma rikici ya barke tsakanin magoya bayan gwamnatin Eritriya da masu adawa da gwamnatin duk a Tel Aviv din. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.