Ba mu shirya shiga kungiyar BRICS ba tukuna - Morocco
Kasar Morocco ta ce har yanzu ba ta gabatar da bukatar shiga kungiyar kasashen BRICS ba, kuma ba za ta halarci taron da za ta gudanar a Afirka ta Kudu ba.
Wallafawa ranar:
Da yake ambato wata majiyar diflomasiyya da ba a bayyana sunanta ba, kamfanin dillancin labaran kasar na MAP ya musanta sanarwar da ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Anil Sooklal ya yi, wanda ya ce a farkon wannan watan kasar Morocco na cikin kasashen da ke neman shiga kungiyar.
Kungiyar kasashe masu tasowa a halin yanzu sun hada da Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu, amma za a tattauna yiwuwar fadada ta a taron kuma Afirka ta Kudu, inda ta ce fiye da kasashe 40 ne suka nuna sha'awar shiga.
Taimakon diflomasiyya da Afirka ta Kudu ke baiwa bangaren Polisario da Aljeriya ke marawa baya, da ke neman kafa kasa mai cin gashin kanta a yammacin Sahara, yankin da Morocco ke dauka a matsayin nata, ya dagula dangantaka tsakanin kasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu