Isa ga babban shafi

Al'ummar Ecuador sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa

A yau lahadi ne kasar Ecuador ke gudanar da zabe na musamman domin zaben sabon shugaban kasa, abin da ya sanya jami’an ‘yan sanda da sojoji cikin taka-tsan-tsan bayan tashin hankalin da ba a taba ganin irinsa ba, ciki har da kisan wani dan takara a wannan watan.

Wata mata da ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka yi a kasar Ecuador ranar 7 ga watan fabrairu, 2021.
Wata mata da ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka yi a kasar Ecuador ranar 7 ga watan fabrairu, 2021. AP - Dolores Ochoa
Talla

‘Yan takarar da ke kan gaba sun hada da wani abokin tsohon shugaban kasar Rafael Correa da ke gudun hijira da kuma wani attajirin da ke da masaniya kan harkokin tsaro wanda ya yi alkawarin yin tsauri kan aikata laifuka.

Hukumomin kasar dai sun tura ‘yan sanda da sojoji sama da 100,000 domin kare kuri’ar da aka kada a zaben.

An kashe dan takara Fernando Villavicencio a ranar 9 ga watan Agusta a lokacin da yake barin wani gangamin yakin neman zabe a Quito, babban birnin kasar ta Kudancin Amurka da aka samu kwanciyar hankali.

Kisan ya dada tsoratar da mutane a kasar da ke fama da matsalar fashi, garkuwa da mutane, kwace, kisa da masana tsaro ke ganin ya zama ruwan dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.