Isa ga babban shafi

'Yan sandan Brazil sun cafke wani mutum da ya yi ikirarin kashe shugaba Lula

'Yan sanda a Brazil sun kama wani mutum da ya ce ya shirya harbin shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, kuma sun kai wani samame kan wani saboda ya yi wa shugaban mai sassaucin ra’ayi barazana ta yanar gizo.

Shugaban kasar Brazil kenan, Luiz Inacio Lula da Silva
Shugaban kasar Brazil kenan, Luiz Inacio Lula da Silva © Ricardo Stuckert/Divulgação
Talla

Wadannan tuhume-tuhume dai na faruwa ne a jihar Para da ke arewacin kasar, inda Lula zai isa nan gaba domin karbar bakuncin taron shugabannin Kudancin Amurka a mako mai zuwa kan kare gandun daji na Amazon.

‘Yan sandan tarayya sun ce sun kama wani mutum a birnin Santarem bayan ya shiga wani kantin sayar da kayan sha a ranar Laraba kuma ya ce ya yi shirin harbin shugaban kasa idan ha rya samu dama.

An kama mutumin ne a ranar Alhamis bayan da wani mutum ya  kai kararsa ga ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun ce mutumin ya shaida wa masu binciken cewa shi manomi ne kuma tsohon mai hakar zinare ne kuma ya amsa laifin da ya taka rawa a tarzomar ranar 8 ga watan Janairu (2019-2022) a Brasilia da magoya bayan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro suka yi.

‘Yan sanda sun ce mutumin ya amsa laifin kutsawa majalisar dokokin kasar, a wannan rana, lokacin da gungun masu tsatsauran ra'ayi suka mamaye ginin, fadar shugaban kasa da kuma kotun koli bayan kayen da Bolsonaro ya sha a zaben daga abokin karawarsa Lula mai shekaru 77.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.