Isa ga babban shafi

An tuhumi Trump kan yunkurin sauya zaben Amurka

Masu gabatar da kara sun tuhumi tsohon shugaban Amurka Donald Trump da laifin yunkurin sauya  sakamakon zaben shugaban kasar na shekarar 2020, domin ci gaba da zama kan mulki, abin da suka bayyana da yunkurin haifar da cikas ga ginshikin dimokaradiyya. 

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump © AP / Matt Rourke
Talla

Tun a jiya Talata lauyoyi suka gabatar wa kotu kundin laifin mai shafuka 45 a birnin Washington, wanda ya yi bayani dalla-dalla akan tuhume-tuhume-tuhume guda hudu da ake yi wa Trump, wadanda wasunsu ke dauke da hukuncin daurin shekaru 20. 

Daga cikin wadannan tuhume-tuhume da Trump ke fuskanta akwai shirya makarkashiyar damfarar Amurka da kuma amfani da karfin kujerarsa wajen kokarin hana hukuma aiki. 

Karo na uku kenan tun daga watan Maris na wannan shekara da lauyoyi ke gabatar da tuhume-tuhumen aikata laifuka daban-daban kan Trump. 

Cikin kundin tuhumar na baya-bayan nan, masu gabatar da kara sun yi zargin cewa Trump ya jajirce wajen kokarin tabbatar da ikirarin da shi kansa ya san ba gaskiya ba ne ta hanyar tursasa manyan jami’an gwamnati, ciki har da mataimakinsa a wacccan lokaci Mike Pence da su sauya sakamakon zaben na 2020.

Daga karshe  kuma ya tunzura magoya bayansa wajen kai hari kan zauren majalisun dokokin Amurka na Capitol a ranar 6 ga Janairu, na  shekarar 2021, a kokarin tsohon shugaban kasar na haifar da cikas ga dimokuradiya da kuma ci gaba da mulki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.