Amurka da Japan da Turai na fuskantar yanayin zafi da basu taba gani ba
Kashen Amurka da Japan da wasu yankunan Turai na fuskantar tsanin zafi da masana yanayi ke cewa zai kai kololuwar da da suka taba gani a litinin mai zuwa, a wani sabon misali dake tabbatar da barazanar dumamar yanayi.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da yanayi a Italiya ta yi hasashen yayin zafin rana zai haura 43 a birnin Roma ranar Talata, inda zai karya tarihin maki 40.5 da suka taba gani a watan Agustan 2007.
Cibiyar kula da yanayi a Girka tace tun daga yau Asabar ake fuskantar zafin da ya kai maki 44 a ma’auninsa, Faransa da Jamus da Spain da Poland ma suna cikin mummnunar yanayin na zafin rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu