Yariman Jordan ya auri 'yar kasar Saudi Arabia
Yariman Jordan Hussein bin Abdullah yau ya auri wata masaniya zaiyane zaiyanen kasa ‘yar kasar Saudi Arabia, Rajwa Al Saif a wani kasaitaccen bikin da akayi wanda ya samu halartar ‘yan gidan sarauta daga sassan duniya.
Wallafawa ranar:
An dai gudanar da wannan bikin ne a fadar Zahran dake birnin Amman ta kasar Jordan, inda aka saba gudanar da bukukuwan auran da suka shafi iyalan masarautar Hashemite, ciki harda auran Sarki Abdallah na biyu da Sarauniya Rania da kuma wanda mahaifinsa Sarki Hussein bin Talal yayi.
An daura auran Yarima Hussein da Rajwa Al Saif wadanda ke da shekaru 28 a gaban ‘yan uwa da kuma baki 140, cikin su harda uwargidan shugaban Amurka, Jill Biden da Yariman Birtaniya da na Wales.
Mahaifin angon, wato Sarki Abdallah mai shekaru 61 a duniya, ya hau karagar mulki ne tun daga shekarar 1999, kuma yana ta kokarin horar da ‘dansa Hussein wajen dabarun mulki da kuma halartar tarurruka da shi, domin ganin ya gaje shi.
Yarima Hussein ya zama mai jiran gado ne tun daga shekarar 2009 bayan mahaifinsa ya karbe mukamin daga ‘dan uwansa Hamzah a shekarar 2004, shekarar da aka zarge shi da yunkurin yiwa Abdallah juyin mulki.
Cikin wadanda suka halarci bikin na yau harda Sarkin Netherlands, Willem-Alexander da Sarauniya Maxima da kuma Sarkin Belgium Philippe da Gimbiya Elizabeth da kuma Yarima Frederick da Gimbiya Mary.
A shekarar da ta gabata, Hussein yayi watsi da sarautar Yarima, bayan ya bayyana cewar manufofin da yake rike da su sun sabawa masarautar ta Jordan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu