Isa ga babban shafi

'Yan majalisar Tarayyar Turai hudu na fuskantar tuhumar karbar rashawa

An tuhumi mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai Eva Kaili, mai ra'ayin gurguzu ta kasar Girka da laifin cin hanci da rashawa tare da tsare ta a gidan yari, bayan da masu binciken Belgium suka gano jaka makare da kudi a gidanta.

Eva Kaili
Eva Kaili © 网络图片
Talla

‘Yan sandan Belgium na gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa masu yiwa Qatar aiki, masaukin baki a gasar cin kofin duniya, da ake zargi da bai wa ‘yan siyasar Turai cin hanci don haifar da tarnaki ga muhawarar manufofin Brussels.

Kaili, wanda ta yi magana a bainar jama'a don nuna goyon bayanta ga sauye-sauyen da Qatar ta yi a baya-bayan nan na ma'aikata, na daya daga cikin mutane hudu da ake zargi da karbar rashawa.

Ofishin mai shigar da kara na Tarayyar Belgium bai bayyana sunayen mutanen hudu ba, sai dai wata majiyar shari'a ta tabbatarwa da AFP cewa Kaili na cikin wadanda ake tuhuma.

Kamen ya biyo bayan wani samame da aka kai a Brussels wanda masu gabatar da kara suka ce an samu tsabar kudi Euro 600,000 kwatankwacin dalar Amurka 630,000.

An cire Kaili daga mukaminta na mataimakiyar shugaban majalisa, musamman na wakiltar Metsola a Gabas ta Tsakiya, amma har yanzu ita mamba ce a kungiyar Tarayyar Turai, kuma za ta ci gaba da samun kariya.

Daga cikin mutane 6 da aka kama a ranar Juma'a, bayan samamen, akalla 'yan sanda 16 suka mamaye tsohon mamba a kungiyar ta EU, Pier-Antonio Panzeri da takwaransa dan kasar Italiya Luca Visentini, babban sakatare a kungiyar kwadago ta kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.