Isa ga babban shafi

Za a dawo da gawar wani dalibi dan Zambia daga Rasha

A gobe Lahadi,za a dawo da gawar wani dalibi dan kasar Zambia da aka dauka aiki a gidan yarin kasar Rasha kafin a kashe shi a lokacin fada a Ukraine, a wata sanarwar da  gwamnatin Zambia ta fitar a yau.

Wasu daga cikin ma'aikatan  kungiyar agajin gaggawa dauke da gawar wani abokin aiki
Wasu daga cikin ma'aikatan kungiyar agajin gaggawa dauke da gawar wani abokin aiki REUTERS/Stringer
Talla

An kashe Lemekhani Nathan Nyirenda, mai shekaru 23 da ya kasance a gidan yari kusa da birnin Moscow, a watan Satumba vayin kasancewa da mayakan Rasha a fagen daga ya rasa ran sa.

Ministan harakokin wajen Zambia Stanley Kakubo ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa, gawar Lemekhani ta isa birnin Moscow a yau asabar, kuma za a dawo da ita kasar Zambia a gobe 11 ga watan Disamba.

A watan da ya gabata ne Zambia ta bukaci Rasha ta yi mata bayani cikin gaggawa game da halin da ya shiga. makonni biyu bayan haka, kungiyar tsaro mai zaman kanta a  Rasha Wagner ta yarda cewa ta dauki matashin a gidan yari, tana mai cewa ya shiga Wagner da son ran sa kafin ya mutu  a matsayin jarumi" a yaki da  Ukraine.

A ranar 22 ga Satumba, ya kasance "daya daga cikin na farko da suka kutsa kai cikin ramukan abokan gaba, ya  nuna jaruntaka in ji shugaban Wagner Evgeny Prigojine.

"Dokokin Rasha sun ba da damar yin afuwa ga fursunoni dangane da ayyukan soji na musamman," in ji ministan Zambia.

Ministan ya kara da cewa, za a tattauna batun biyan diyya ga dangi na wannan dalibi a kan lokaci..

A cewar Zambia, matashin yana karatun injiniyan nukiliya ne a cibiyar nazarin kimiyyar injiniya da ke birnin Moscow. An yanke masa hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari a watan Afrilun 2020 saboda samun sa da miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.