Isa ga babban shafi

'Yan sandan Europol sun cafke gungun masu safarar hodar iblis a Dubai

'Yan sandan kasa da kasa sun cafke masu sarrafawa da safarar  kusan kashi daya bisa uku na hodar iblis a Turai, inda suka kama mutane 49 a kasashe daban-daban, ciki har da manyan mutane shida da ake zargi a Dubai.

Galibin mutanen da aka cafke sun fito daga kaashen Belgium Faransa da Spain
Galibin mutanen da aka cafke sun fito daga kaashen Belgium Faransa da Spain Europol
Talla

Wani faifan bidiyo da rundunar ta Europol ta fitar ya nuna jami’ai da suka hada da wasu daga Hukumar Yaki da Muggan Kwayoyi ta Amurka da na Spain suna kamen wadanda ake zargi tare da kwace wasu manyan motoci na alfarma da wasu makudan kudade da aka boye.

An cafke mutum goma a kasar Belgium, shida a faransa, sannan 13 a Spain. Bugu da kariu akwai mutum 14 da aka cafke a shekarar 2021 a Netherlands, duk dai karkashin aikin rundunar na farautar masu aikata wannan ta’asar.

Kamen mutanen da aka yi daga ranar 8 zuwa 19 ga watan Nuwamba shi ne mafi tasiri na baya-bayan nan da aka yi a nahiyar Turai, wanda hakan ya biyo bayan nadar bayanan sirri da ‘yan sandan su ka yi ta wayar salula, game da yadda kungiyoyin masu aikata laifuka suka shirya.

Yawancin miyagun kwayoyin ko kuma hodar ibilis din da ake hada-hadar su, ana shigowa da su ne daga Kudancin Amurka ta tashar jirgin ruwa na Rotterdam da Antwerp, ko da yake bayanai sun ce wani lokacin masu irin wannan kasuwanci kan yi amfani da Afirka ta Kudu wajen fitar da su.

Sai dai masu gabatar da kara na Holland sun ce za su bukaci a mika mutanen biyu daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cikin wata sanarwa da rundunar mai hedikwata a birnin Hegue ta fitar ta ce, shugaban masu safarar miyagun kwayoyin, dan kasar Birtaniya, ya tsere zuwa Dubai bayan yunkurin kama shi a kasar Spain, inda ya ci gaba da bawa yaransa umarnin yadda za su gudanar da haramtattun kasuwanci.

Ana shigo da hodar iblis ne daga Panama da ke tsakiyar Amurka, kuma mai safarar ta dan kasar Panama shi ma yana zaune a Dubai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.