Isa ga babban shafi

Amurka ta ci tarar Boeing dala miliyan 200 kan hadarin jirginsa kirar MAX 737

Gwamnatin Amurka ta ci tarar kamfanin kera jiragen saman Boieng Dala miliyan 200 saboda gabatar da bayanan karya dangane da jirgin sa kirar MAX 737 wanda yayi hadari sau biyu, ya kuma haddasa asarar rayukan jama’a.

Tambarin kamfanin jiragen sama na Boeing da ke kasar Amurka.
Tambarin kamfanin jiragen sama na Boeing da ke kasar Amurka. AFP/File
Talla

Hukumomin Amurka sun ce Kamfanin ya amsa kuskuren sa, kuma ya amince ya biya tarar kudin na Dala miliyan 200.

Wannan tarar ta biyo bayan hadarin da jirgin ya yi da fasinjojin Indonesian Airline cikin watan oktobar shekarar 2018 da kuma Ethiopian Airlines a watan Maris na shekarar 2019, inda mutane kusan 350 suka mutu.

Wadannan hadura guda biyu sun sanya kamfanonin jiragen sama da dama a sassan duniya, daina amfani da jirgin Boeing samfurin MAX 737 a zirga-zirgarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.