Isa ga babban shafi

Zan daina tafiye-tafiye ko na yi murabus baki ɗaya - Fafaroma Francis

Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis ya sanar da shirin takaita ziyarce-ziyarce da yake yi zuwa kasashen duniya, ko ma ya yi ritaya baki daya saboda yana bukatar hutu a cewarsa.

Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis
Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis AFP - VINCENZO PINTO
Talla

Da yake zantawa da manenma labarai bayan ziyarar kwanaki shida da ya kai kasar Canada Paparoman mai shekaru 85 da ake ganin ya fara dogaro da keken tura marasa lafiya saboda ciwon guiwa, ya ce "Ba ya jin zai iya ci gaba da tafiye-tafiye kamar yadda ya saba.

Benedict

Wannan dai ba shi ne karon farko da Francis ke bayyana yiwuwar yin koyi da wanda ya gada Benedict na 16 ba, wanda ya yi murabus saboda rashin lafiyarsa a shekarar 2013, kuma yanzu haka yana zaune cikin nutsuwa a birnin Vatican.

A shekarar  2014, shekara guda a kan karagar mulkinsa, Francis ya shaida wa manema labarai cewa idan har lafiyarsa ta kawo masa cikas a matsayinsa na Paparoma, zai yi tunanin sauka daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.