Isa ga babban shafi

Sashin Hausa na RFI ya cika shekaru 15 da kafuwa

Yau Asabar sashin Hausa na RFI ke bikin cika shekaru 15 da fara gabatar da shirye shirye, kafar da a yanzu ke da miliyoyin masu sauraro, baya ga masu bibiyarmu da shafin Intanet.

Sashin Hausa na RFI na murnar cika shekaru 15 da kafuwa.
Sashin Hausa na RFI na murnar cika shekaru 15 da kafuwa. © Studio graphique FMM
Talla

A rana mai kamar ta yau ce dai wato 21 ga watan Mayu na shekarar 2007, Faransa ta bude sashen hausa na RFI don yada shirye-shiryen da harshen mafi girma a nahiyar Afrika, wanda kuma ya zama sashi na farko da kasar ta bude da wani yare a Nahiyar Afrika.

Sashin Hausa na RFI ya cika shekaru 15 da fara yada labarai.
Sashin Hausa na RFI ya cika shekaru 15 da fara yada labarai. © RFI Hausa

An kafa gidan ne a karkashin marigayiya Lanni Smith, wadda ta kafa tarihin zama shugaba ta farko ga sashin na Hausa na gidan Rediyon na RFI.

Bayan marigayiya Lanni, Emmanuel D'abzac ne ya karbi jagorancin, inda bayan kusan shekaru 2 kuma, Madam Julie Vandal ta karbi ragamar shugabancin sashin Hausar na gidan rediyon RFI, kafin daga bisani Mr Robert Minangoy ya cigaba da jagoranci har zuwa watan Nuwamban shekarar 2021, lokacin da shugaba ta yanzu Sophie Bouillon ta karbi ragamar jagorancin gidan.

A yanzu haka Bashir Ibrahim Idris ne babban Editan gidan rediyon na RFI Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.