Isa ga babban shafi
RFI

‘‘RFI hausa ya cim-ma manufofin kafa shi’’

Sarakuna da shugabanin al’umma da masu sauraro daga sassa daban-daban na duniya na ci gaba da aikon sakon ta ya murna ga RFI hausa da ya cika shekaru 10 da kafuwa.

Laurent Polonceaux a bikin cikar RFI hausa shekaru 10 da kafuwa
Laurent Polonceaux a bikin cikar RFI hausa shekaru 10 da kafuwa
Talla

RFI hausa ya gudanar da bikin cika shekaru 10, kuma masana da masu sauraro sun yi nazari kan ci gaban da aka samu da kuma bada shawarwari kan gyaran da suke so ayi.

Daga cikin manyan baki da suka halarci wannan biki da aka gudanar a jiya Lahadi akwai jakadan karamin ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Lagos Laurent Polonceaux, wanda ke cewa a cikin shekaru 10 da kaddamar da shirye-shiryensa, sashen hausa na rfi an cim-ma manofofin da suka sa aka kafa shi.

Mista Polonceaux ya ce babu shaka ana kara samun ci gaba sosai, kuma wasu daga cikin alamomi da ke kara tabbatar da hakan sun hada da kara yawan lokacin yada shirye-shiryen rfi hausa da wasu mintuna 30 a kowace rana.

''A gaskiya kirkiro sashen hausa na rfi ya taimaka wajen samar da karin masu sauraren rfi a maimakon Faransanci da kuma sauran harsuna da ya ke yada shirye-shiryensa''.

Mista Polonceaux ya kuma bayanna cewa wani abin ci gaba shi ne yadda kirkiro wannan sashen ke kara taka rawa wajen kyautata alaka tsakanin harsuna biyu wato harshen Faransanci da kuma harshen Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.