Isa ga babban shafi

An sake tisa keyar Fariba Adelkhah gidan yari a Iran

A yau lahadi ,daya daga cikin ma’aikatan dake aiki da hukumomin shara’a na kasar Iran ya sheidawa kamfanin dilanci labaren kasar cewa an sake tisa keyar Ira gidan yari,bisa  tuhumar ta da rashin bin ka’idojin da aka gindaya mata bayan saki talala da aka yi mata.

Fariba Adelkhah, na tsare a kasar Iran
Fariba Adelkhah, na tsare a kasar Iran © Capture d'ecran Sciencespo
Talla

Fariba mai shekaru 62 ta kasance a tsare tun a watan yuni na shekara ta 2019,wace kotu ta zartaswa da hukunci dauri na shekaru  biyar bisa zargin ta da cin amanar kasa.

 Fariba Adelkhah dake tsare a kasar Iran
Fariba Adelkhah dake tsare a kasar Iran Thomas ARRIVE Sciences Po/AFP/File

Kasashen Duniya da masu kare hakokkin bil Adam na ci gaba da kira ga hukumomin Teheran na ganbin sun salami wannan Fariba  da ta yi fice a fanin bincike,Shugaban Faransa Emmanuel Macron  ya kalubalanci matakin hukumomin Iran,tare da bayyana cewa Faransa na ci gaba da goyan bayan Fariba Adelkhah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.