Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta fara biyan diyyar fasinjojin jirgin saman da sojojinta suka harbo

Iran ta fara biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutu a lokacin da sojojinta suka harbo wani jirgin saman fasinja na kasar Ukraine shekaru biyu da suka gabata.

Jami'an tsaro da ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Crescent a wurin da jirgin saman Ukraine International Airlines ya yi hadari bayan tashinsa daga filin jirgin saman Imam Khomeini na Iran, a wajen birnin Tehran, a ranar 8 ga Janairu, 2020.
Jami'an tsaro da ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Crescent a wurin da jirgin saman Ukraine International Airlines ya yi hadari bayan tashinsa daga filin jirgin saman Imam Khomeini na Iran, a wajen birnin Tehran, a ranar 8 ga Janairu, 2020. Nazanin Tabatabaee/WANA via REUTERS
Talla

Cikin wata sanarwa kan cika shekaru biyu da fuskantar mummunan hatsarin, ma'aikatar sufurin Iran ta ce tuni ta aike da kudaden diyyar da yawansu ya kai dala dubu dari da hamsin-hamsin ga wasu daga cikin iyalan wadanda hatsarin kakkabo jirgin ya rutsa da su, a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin ta da Amurka.

A ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2020, dakarun Iran suka harbo jirgin saman fasinjan Ukraine jim kadan bayan tashinsa daga Tehran, inda daukacin mutane 176 da ke cikinsa suka mutu, yawancinsu 'yan Iraniyawa da Canada.

Wasu daga cikin iyalan fasinjojin jirgin saman Ukraine da sojojin Iran suka harbo a watan Janairun shekarar 2020.
Wasu daga cikin iyalan fasinjojin jirgin saman Ukraine da sojojin Iran suka harbo a watan Janairun shekarar 2020. AP - Efrem Lukatsky

Bayan kwanaki uku da faruwar lamarin ne sojojin Iran suka amsa laifin kakkabo jirgin bisa kuskure, wanda ke kan hanyar zuwa Kiev babban birnin kasar Ukraine daga Teheran.

A halin da ake ciki dai, jami'an gwamnatin Ukraine da na Canada sun yi kakkausan suka ga sanarwar Iran akan fara biyan diyyar fasinjojin da suka mutu, suna masu cewa bai kamata a warware batun ta hanyar sanarwar bai daya ba.

Tun cikin watan Nuwamban da ya gabata, ma’aikatar shari’ar Iran ta bayyana gurfanar da wasu sojoji 10 a Tehran, dangane da harbo jirgin saman na Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.