Isa ga babban shafi
BULGARIA

Hadarin mota ya kashe mutane 45 a Bulgaria

‘Yan Sanda a kasar Bulgaria sun ce mutane 45 suka mutu sakamakon wani kazamin hadarin motar da aka samu a cikin kasar.

Kan titin da hadarin ya faru a Bulgaria
Kan titin da hadarin ya faru a Bulgaria Dimitar Kyosemarliev AFP
Talla

Nikolay Nikolov, shugaban hukumar agajin gaggawa da kare lafiyar jama’a a ma’aikatar cikin gidan kasar yace mutanen 45 sun rasu ne sakamakon hadarin da ya ritsa da su akan hanyar Sofia cikin dare, kuma ya zuwa yanzu ba’a iya tantance abinda ya haifar da hadarin ba.

Jami’in yace 7 daga cikin fasinjojin motar sun tsira da ran su, kuma 12 daga cikin wadanda ke cikin motar yara ne kanana da suka taso daga Santabul dake kasar Turkiya zuwa Skopje dake Arewacin Macedonia.

Firaminista Zoran Zaev wanda ya bayyana kaduwar da hadarin, yace watakila fasinjojin mutanen kasar sa ne.

Zaev ya shaidawa kafar talabijin ‘din kasar Nova cewar, basu da tabbacin cewar mutanen da suka mutu sun fito ne daga Arewacin Macedonia, amma ganin motar su na dauke da lambar kasar suna daukar su a matsayin ‘yan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.