Isa ga babban shafi
SUFURIN-JIRAGEN-KASA

Jamus ta kaddamar da jiragen kasa masu sarrafa kan su

Yau Kasar Jamus ta kaddamar da jiragen kasa masu sarrafa kansu ba tare da matuka ba wanda kamfanin Deutsche Bahn da kamfanin Siemens suka gabatar a birnin Hamburg.

Irin samfurin jiragen da Deutsche Bahn ke kerewa
Irin samfurin jiragen da Deutsche Bahn ke kerewa AFP/File
Talla

Kamfanonin biyu sun bayyana jiragin a matsayin gagarumar ci gaban da za’a sanya su akan hanyar birnin S-Bahn, kuma ana saran daga watan Disamba mai zuwa su fara jigilar fasinjoji akan layukan dogon da ake amfani da su yanzu haka.

Wasu manyan biranen duniya irin su Paris na da jiragen dake zirga zirga a cikin garuruwan su da suma suke saffara kan su, yayin da wasu tashonin jiragen sama ke amfani da kananan jiragen kasa dake jigilar fasinjoji tsakanin tasha zuwa tasha.

Kamfanin Siemens da Deutsche Bahn sun bayyana wannan aiki na su a matsayin irin sa na farko, kuma yana daga cikin aikin inganta jiragen kasan da aka ware Dala miliyan 70.

Shugaban Deutsche Ban Richard Lutz yace sabbin jiragen masu sarrafa kan su za su ci gaba da aiki ba tare da an gina musu sabbin hanyoyi ba.

Shi kuwa shugaban kamfanin Siemens Roland Busch cewa yayi suna inganta harkar sufurin jiragen kasa daidai da zamani, kuma zasu iya kwashe kashi 30 na fasinjoji da ake da su yanzu haka a Jamus kuma a cikin lokaci.

Kamfanin yace duk da yake jirgin zai dinga sarrafa kan sa, zasu sanya direba a ciki domin sanya ido akan fasinjoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.