Isa ga babban shafi
Faransa-Australia

An ci amanar Faransa a cinikin jirgin ruwa- Von der Leyen

Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen ta ce sam ba a yi wa Faransa adalci ba, a batun cinikayyar jirgin ruwan karkashin teku da ta kulla da Australia, tana mai jadadda cewa hakan tamkar cin amana ne.

Shugabar hukumar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugabar hukumar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron. LOUISA GOULIAMAKI AFP
Talla

Tun makon da ya gabata ne, cacar-baka ta barke tsakanin Faransa da Amurka sakamakon yadda Faransar ke zargin Amurka da yi mata kutungwila wajen kwace cinikayyar jirgin karkashin tekun.

A cewar Ursula Von der Leyen Tarayyar Turai ba za ta amince a yi wa wata mambarta makamancin wannan cin mutunci ba.

Tun da fari dai Faransa ce ta kulla yarjejeniya da kasar Australia wajen sayar mata da jirgin ruwan karkashin teku, amma kwatsam sai labarin janye yarjejeniyar ya bulla.

Australia ta sanar da janye yarjejeniyar da ta kulla da Faransa, bayan da tuni Faransan ma ta fara aikin samar da jirgin, abinda ta ce ba mai sabuwa ba ne.

Bayan da Australia ta janye yarjejeniyar ta kuma kulla makamanciyar ta da Amurka, abin da tarayyar Turai ta ce karara cin dunduniyar Faransa ne da kuma yi mata zagon kasa.

Sai dai tuni shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bukaci tattaunawa da na Faransa don shawo kan lamarin, da ka iya wargaza alakar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.