Isa ga babban shafi
Amurka

An cika shekaru 20 da kai hare-haren 9/11

Yau Asabar ake cika ​shekaru 20 da kai harin ta'addancin ranar 11 ga Satumban shekarar 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 3 a Amurka.

Hayaki na tashi daga tagwayen hasumiyar Cibiyar Ciniki ta Duniya bayan harin kunar bakin da aka kai musu a ranar 11 ga Satumba, na shekarar 2001 a birnin New York.
Hayaki na tashi daga tagwayen hasumiyar Cibiyar Ciniki ta Duniya bayan harin kunar bakin da aka kai musu a ranar 11 ga Satumba, na shekarar 2001 a birnin New York. AP - Richard Drew
Talla

A waccan lokacin dai 'yan ta'adda 19 masu alaka da kungiyar al Qaeda ne suka kwace jiragen sama 4 tare da kai hare-haren kunar bakin wake kan tagwayen hasumiyar Cibiyar Ciniki ta Duniya da ke birnin New York da jirage 2, sai kuma ma’aikatar tsaro ta Pentagon a birnin Washington, yayin na hudunsu ya fadi a Shanksville, da ke Pennsylvania.

Yayin alhinin tunawa da wadanda suka mutu a yau, za a ziyarci dukkanin wuraren da hare-haren kunar bakin waken suka shafa domin karrama mutanen da tashin hankalin ya rutsa da su.

Garba Sulaiman Krako Saminaka mazaunin Amurka ne da ya tsallake rijiya da baya yayin hare-haren na 9/11, ya kuma hari, yayin zantawa da sashin Hausa na RFI ya ce shi ganau ne ba jiyau ba.

00:59

Garba Sulaiman Krako Saminaka da ya tsallake rijiya da baya yayin hare-haren na 9/11 a Amurka

Hare-haren na 9/11 sun sauya manufofin Amurka da kuma janyo matakan da ta dauka don yakar ta'addanci a zamanin shugabancin George W. Bush, abinda ya kai ga afkawa kasar Afghanistan da yaki, saboda mafakar da gwamnatin Taliban ta baiwa shugaban Al Qaeda Osama Bin Laden a waccan lokaci.

Wani rahoto da aka wallafa a Talatar da ta gabata ya nuna cewa, kawo yanzu mutane akalla dubu 3 da 900 suka mutu sakamakon fama da cutukan da suka gamu da su dalilin harin na 11 ga watan Satumba, adadin da ya zarce na wadanda suka mutu a ranar da lamarin ya auku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.