Isa ga babban shafi
Birtaniya-Masarauta

Mijin Sarauniyar Ingila ya mutu

Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya mutu yana da shekaru 99 a duniya kamar yadda fadar Buckingham ta sanar a yau Jumma’a.

Marigayi Yariman Birtaniya Philip ya mutu yana da shekarub 99
Marigayi Yariman Birtaniya Philip ya mutu yana da shekarub 99 REUTERS - POOL New
Talla

Mutuwar Wazirin na Edinburg na a matsayin babban rashi ga Sarauniyar mai shekaru 94 wadda a baya ta  bayyana shi a matsayin ginshiken da ya tsaya mata a tsawon shekaru.

Ma'auratan sun kafa tarihin zama mafi dadewa suna mulkin Birtaniya
Ma'auratan sun kafa tarihin zama mafi dadewa suna mulkin Birtaniya AP - Leslie Priest

A ranar 16 ga watan Fabairu ne aka kwantar da marigayin a asibiti kafin ya koma gida bayan share tsawon wata guda yana jinyar ciwon zuciya.

Mutuwarsa  na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da bikin cikarsa  shekaru 100 da haihuwa a cikin watan Yuni mai zuwa.

Yariman ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, wato shekaru biyar kafin ta dare kan gadon sarautar Ingila, yayin da  ma’auratan biyu suka kafa tarihin zama masu mulki mafi dadewa kan karaga a tarihin Birtaniya.

Yarima Philip tare da matarsa Sarauniya Elizabeth cikin kuruciya
Yarima Philip tare da matarsa Sarauniya Elizabeth cikin kuruciya AP - Kathy Willens

Ma’auratan biyu na da yara hudu da jikoki takwas da kuma tattaba-kunni 10.

Sanarwar da fadar Buckingham ta fitar ta ce, Yariman ya mutu cikin kwanciyar hankali a wannan safiyar a gidan sarautar Windsor.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.