Isa ga babban shafi
Jordan

An sanya tsohon mai jiran gadon sarautar Jordan karkashin daurin talala

Tsohon yarima mai jiran gadon sarautar Jordan Hamza bin Hussein ya ce jami’an tsaron kasar sun yi masa daurin talala a gidansa, sai dai ya musanta zargin da ake masa da hannu wajen shirya zagon kasa ga gwamnatin dan uwansa Sarkin kasar ta Jordan Abdallah na 2, da ya zarga da laifukan rashawa.

Tsohon Yarima mai jiran gadon Sarautar kasar Jordan Hamza bin Hussain, yayin sanya hannu kan takardar daurin aurensa.
Tsohon Yarima mai jiran gadon Sarautar kasar Jordan Hamza bin Hussain, yayin sanya hannu kan takardar daurin aurensa. © Pinterest
Talla

Cikin wani hoton bidiyo, Yarima Hamza yace babban Hafsan sojin kasar Jordan da kansa ne ya shaida masa matakin daurin talalar da aka dauka kansa.

Yariman ya kuma ce a halin da ake ciki jami’an tsaro sun kame wasu makusantansa, zalika an janye masu tsaron lafiyarsa tare da katse masa intanet da layukansa na wayoyin hannu.

Tsohon mai jiran gadon Sarautar dai na cigaba da musanta hannu wajen shiryawa Jordan zagon kasan da kai ga fuskantar matsalolin tafiyar da gwamnati da kuma rashawar da ta yi mata katutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.