Isa ga babban shafi
Amurka

Wasu tsageru na shirin kai wa Majalisar Amurka hari

An karfafa matakan tsaro a harabar ginin Majalisar Dokokin Amurka na Capitol bisa fargabar yiwuwar kai wa ginin hari a wannan Alhamis.

Jami'an tsaron Amurka sun ja daga a harabar ginin Majalisar Dokokin Kasar na Capitol
Jami'an tsaron Amurka sun ja daga a harabar ginin Majalisar Dokokin Kasar na Capitol Andrew CABALLERO-REYNOLDS AFP
Talla

Daukar matakin na zuwa ne bayan bayanan sirri sun nuna cewa, wani gungun tsageru ya kitsa kaddamar da farmakin a wannan rana ta 4 ga watan Maris, ranar da bisa al’ada aka saba rantsar da shugabannin Amurka.

Tsagerun sun yi amanna cewa, yau Alhamis na a matsayin ranar da tsohon shugaban kasar Donald Trump zai koma cikin fadar White House don fara sabon wa’adin mulkin kasar duk da cewa, ya sha kayi a zaben da Joe Biden ya doke shi a bara.

Tuni Majalisar Wakilan Kasar ta soke zamanta na yau, amma Majalisar Dattawa za ta ci gaba da al’amuranta.

Baranazar na zuwa ne watanni biyu  da magoya bayan Trump suka kutsa cikin ginin  na Capitol  a cikin wata tarzoma wadda ta yi sanadiyar salwantar rayukan mutane akalla biyar cikinsu har da jami'in 'yan sanda.

Lokacin da magoya bayan Trump suka far wa ginin  Majalisar Dokokin Kasar na Capitol a cikin watan Janairu.
Lokacin da magoya bayan Trump suka far wa ginin Majalisar Dokokin Kasar na Capitol a cikin watan Janairu. REUTERS - SHANNON STAPLETON

Magoya bayan sun keta shingen ginin ne a daidai lokacin da ‘yan Majalisar Dokoki ke  gudanar da zaman tabbatar da nasarar shugaba Biden a zaben watan Nuwamba, zaben da Trump ya ki amibncewa da shan kayi.

Wannan harin ya girgiza ginshiken demokuradiya da Amurka ta kafa a duniya. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.