Isa ga babban shafi
Cancer-Coronavirus

Coronavirus ta haddasa gagarumin koma baya a yaki da Cancer- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan yadda yaki da cutar Coronavirus ke shirin haddasa nakasu a kokarin da ake na bayar da kulawa ga masu fama da cutar Cancer a sassan Duniya.

Kowacce kasa 1 cikin 3 a Duniya ta fuskanci mummunan koma baya a yaki da Cancer.
Kowacce kasa 1 cikin 3 a Duniya ta fuskanci mummunan koma baya a yaki da Cancer. Crédits : The Washington Post / Contributeur / Getty Images
Talla

Shugaban hukumar WHO shiyyar Turai Hans Kluge a jawabinsa kan ranar kula da masu ciwon Cancer ta Duniya, ya ce duk daya cikin kasashen Turai 3 yanzu na fuskantar babban tashin hankali wajen kula da masu cutar ta Cancer.

A cewar jami’in, hankulan kasashen Duniya ya karkata kacokan wajen yaki da Coronavirus wanda ya tilasta kasashe 53 da ke cikin WHO da kaso mai yawa a tsakiyar Asiya da kuma Turai fuskantar babban kalubale wajen kula da masu Cancer sakamakon yadda ko dai sashen da aka warewa cutar ya fuskanci nakasu ko kuma ya durkushe baki daya.

Sanarwar da Kluge ya fitar yau Alhamis ya ce kasashe da dama ciki har da masu matukar arziki sun fuskanci karancin magunguna kula da masu cutar ta Cancer yayinda wasu kuma suka kawar da kai daga sashen kula da masu Cancer dungurugum tare da bayar da fifiko ga yaki da Coronavirus.

A kasashen Netherlands da Belgium yayin kullen da kasashe suka gani a 2020 masu fama da Cancer sun fuskanci karancin kulawa daga kashi 40 zuwa 30 yayinda tsarin kula da Cancer a Kyrgyzstan ya ragu zuwa kashi 90, batun Mr Hans Kluge ke bayyanawa da babban abin damuwa a yaki da cutar ta Cancer a Duniya.

Haka zalika Mr Kluge ya bayyana damuwa kan yadda hasashe ke nuna yiwuwar samun karuwar mace mace sanadiyyar Cancer a Birtaniya kadai da kashi 15 yayinda za a samu karuwar masu fama da Cancer mama da kashi 9 nan da shekaru 5 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.