Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na zagon-kasa ga shirin mika mulki ga Biden

Zababben shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden na ci gaba da shirye-shiryen karbar mulki a cikin watan Janairun sbuwar shekara a daidai lokacin da shugaba Trump ke daukar matakan gurgunta shirin mika mulki bayan ya ki amincewa da shan kaye.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Brendan Smialowski / AFP
Talla

Biden na ci gaba da nuna ko-in-kula kan matsayin abokin hamayyarsa Trump na kin amincewa da sakamkon zaben shugaban kasar, duk da cewa hukumomin kasar na gargadin cewa, matakin Trump ka iya haifar da hadarin gaske.

Tun bayan da ya yi ikirarin tafka magudi a zaben na farkon watan nan, shugaba Trump ya toshe duk wata kafa da Biden zai samu muhimman bayanan karbar mulki da kuma hana bada kudin aiwatar da shirin, matakin da wasu manyan mukarraban gwamnatin Republican suka mara wa baya.

A baya-bayan nan zababben shugaba Biden ya bayyana matakin Trump na kin amincewa da shan kaye a matsayin abin kunya, sai dai ya yi ikirarin hakan bai zai haifar da cikas ga shirinsa na karbar mulki nan da ranar 20 ga watan Janairu ba. Kazalika nan gaba kadan shugaba Trump din da sauran mukarrabansa za su saduda a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.