Isa ga babban shafi
RFI

Sashin Hausa na gidan rediyon RFI ya cika shekaru 13 da kafuwa

Yau Laraba Sashin Hausa na gidan rediyon RFI mallakin kasar Faransa ya cika shekaru 13 da soma yada labarai a fadin duniya.

RFI Hausa ta cika shekaru 13 da soma yada labarai.
RFI Hausa ta cika shekaru 13 da soma yada labarai. RFI Hausa
Talla

RFI Hausa daya ne daga cikin sassan harsuna daban daban da babbar tashar gidan rediyon na Faransa da aka fi sani a turance da ‘Radio France International’ ke watsa labarai da sauran shirye-shirye cikinsu.

A ranar Litinin 21 ga watan Mayu shekarar 2007, Sashin Hausa na RFI ya soma yada labarai kai tsaye daga hedikwatarsa dake birnin Legas a Najeriya.

An kafa gidan ne a karkashin marigayiya Lanni Smith, wadda ta kafa tarihin zama shugaba ta farko ga sashin na Hausa.

Bayan marigayiya Lanni, Emmanuel D'abzac ne ya karbi jagorancin, bayan kusan shekaru 2, Madam Julie Vandal ta karbi ragamar shugabancin sashin Hausar na gidan rediyon RFI.

A karkashin shugabancin Julie ne gidan rediyon na RFI Hausa ya cika shekaru 10, daga nan ne kuma shugaba mai ci a yanzu, Mr Robert Minangoy ke cigaba da jagoranci har zuwa wannan lokaci.

A yanzu haka Bashir Ibrahim Idris ne babban Editan gidan rediyon na RFI Hausa, yayinda Garba Aliyu Zaria yake a matsayin mataimakinsa.

A kowa ce safiya akwai shirye-shirye guda biyu daga karfe 7 zuwa 7:30 da kuma 8 zuwa 8:30 agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da Chadi.

Sai kuma shirin yammaci da yake shafe awa guda, daga karfe 5 agogon Najeriya da Nijar zuwa karfe 6.

Sashin Hausa na RFI ya shahara wajen kawo labarun duniya daga sassa daban daban cikin kankanin lokacin da bai wuce mintuna 10 zuwa 12 ba, gami da watsa shirye-shirye da dama da suka shafi Ilimi, Noma, Muhalli, Siyasa, wasanni, Lafiya, Tattalin arziki da kuma Al’adu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.