Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Hanyoyin da ake sauraren RFI Hausa a Salula da Ipad da Andriod

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi ya yi bayani ne akan sabbin hanyoyin da ake sauraren sashen hausa na Radiyo Faransa RFI da suka hada hanyar wayoyin Salula Android da waya kirar Apple da Ipad.

Wayar Android ta zamani mai amfani da Intanet
Wayar Android ta zamani mai amfani da Intanet RFI
Talla

Duk da cewa wasu suna ganin akwatin Rediyo da ake sauraren labarai ya zama kamar tsohon yayi ta la’akari da ci gaban fasaha da ake samu ta hanyoyi daban daban da ake bi a saurari labarai daga tasoshin Rediyo.

Ya kamata ace Rediyo ya kau a zamanin nan saboda samuwar kafar Telebijin da samuwar wayoyon zamani na hannu irinsu smart phones da Walkman da dai sauransu amma har yanzu Rediyo yana nan da matsayinsa musamman ta bangaren karfin tattalin arziki tsakanin ma’abota sauraren labarai.

Sai dai a zamanin nan akwai hanyoyi da ke goyayya da Radio da ake bi wajen sauraren labarai.

Sashen hausa na Radiyo Faransa wanda ya fara yada shirye shiryensa da harshen hausa shekaru 7 da suka gabata, akwai sabbin hanyoyi da gidan Radiyon na Faransa ya samarwa masu saurare saboda tafiya da ci gaban fasaha a zamanin nan.

Wadatuwar samun wayoyin hannu masu hade da Intanet ya sa yanzu mutum ba sai ya lalabi akwatin rediyonsa ba domin sauraren labarai muddin wayarsa ta salula ko kwamfutarsa na hade intanet.

Masu waya Andriod da Apple an tanadar masu hanyar sauraren labaran RFI kai tsaye da kuma duk lokacin da suke so a rumbun manhajojinsu ta App Store. Haka kuma sauran nau’o’in wayoyi suna iya shiga shafin Intanet www.hausa.rfi.fr domin saurare kai tsaye idan kuma ba su da lokaci suna iya saurare duk lokacin da suke so..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.