Isa ga babban shafi
China

An sauya wa cutar Coronavirus suna bayan ta yi barna

Gwamnatin China ta ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da Coronavirus ya kai 1,113 bayan an samu sabbin mamata 97 a jiya Talata, yayin da  mutanen da suka kamu da cutar suka zarce 44,000. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta sauya wa cutar suna zuwa COVID-19 a taron masana da ta yi a birnin Geneva.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus a birnin Geneva
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus a birnin Geneva Fabrice COFFRINI / AFP
Talla

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi wa manema labarai bayani game da cutar, inda ya ce daga 'Corona Virus' da kuma 'Disease' aka samu CONVID-19, kuma lamba ta 19  na nufin shekarar 2019, wato shekarar da aka gano cutar.

Dokar Hukumar Lafiya ta Duniya da aka yi a shekarar 2015 ta hana amfani da sunan Ebola ko Zika, wato garin da cuta ta samo asali wajen ambaton cutar.

Hukumar ta kuma bukaci a guji danganta nau’ukan cutuka da dabbobi, duba da yadda hakan ke janyo rudani, kamar yadda aka danganta cutar H1N1 da aladu, lamarin da ya yi mummunar tasiri ga kamfanonin da ke sarrafa nama.

Hukumar ta kuma haramta amfani da sunayen mutane kamar masana kimiyyar da suka gano cutar, ko kuma wanda aka samu cutar a tattare da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.