Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya mayar da martini kan yunkurin tsige shi

Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da kakkausan martani ga shugabar Majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi wadda ta nanata shirin aiwatar da tsige Shugaban daga mulki bayan kwararan shaidun da ke tabbatar da yadda ya karya tanadin kundin tsarin mulkin kasar. 

Shugaba Donald Trump na Amurka.
Shugaba Donald Trump na Amurka. REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Yayin zaman Majalisar Kasar ta Amurka a jiya Alhamis bayan tattara bayanan kwararru a fannin shari'a da kuma tabbatar da hujjojin da ke nuna shugaban kasar Donald Trump ya karya dokokin kundin tsarin mulki, Nancy Pelosi ta bukaci majalisa ta rubuta takaddar tsige shugaban.

Sai dai Donald Trump cikin martanin da ya mayar mintuna kalilan bayan kalaman na Pelosi ya ce hukuncin zai zamo babban abin kungiya ga shugabar dama Jam'iyyarta ta Democrat baki daya.

Cikin Maratanin na Trump ya sake nanata cewa ko kadan baya da hannu kan zargin da ake masa na yiwa kundin tsarin mulkin kasar karan-tsaye, inda a bangare guda ya ce a shirye ya ke ga duk wani kutun-kutun da Majalisar ke kokarin kitsawa.

Yanzu haka dai ana ci gaba da zaman dakon abin da zai je ya zo a Majalisar mai rinjayen wakilan jam'iyyar Democrat da ke matsayin babbar jam'iyyar adawa ga Republican ta shugaba Donald Trump.

Ko a ranar 24 ga watan Fabarairun shekarar 1868 sai da Majalisar ta Amurka ta tsige shugaban kasar na wancan lokaci Andrew Johnson bayan samunsa da manyan laifuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.