Isa ga babban shafi
Amurka

Democrat ta zurfafa shirinta na tsige Trump

‘Yan Jam’iyyar Democrat sun zayyana taswirar tsige shugaban Amurka Donald Trump daga karagar mulki a hukumance, a daidai lokacin da suke tattara karin hujjoji kan wata haramtacciyar ganawa da shugaban ya yi da takwaransa na Ukraine domin bunkasa tagomashinsa a zaben 2020.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis
Talla

A can baya dai, wani sojan Amurka da ya lashe lambar yabo, ya shaida wa masu bincike na Majalisar Dokokin Kasar cewa, ya ga shugaba Trump da wani babban jami’in diflomasiya na matsin lamba kan Ukraine da zummar bata sunan abokin hamayyarsa ta siiyasa, Joe Biden.

A ranar Laraba ma, wasu jami’ ai uku na wata Ma’aikatar Amurka, sun gabatar da karin hujjoji da ke tabbatar da zargin da ake yi wa Trump.

A halin yaznu, masu binciken sun ajiye ranakun da za su karbi shaidun wasu karin mutane uku, cikinsu kuwa har da tsohon mai bai wa Trump shawara kan tsaro wato John Bolton, wanda ake kyautata zaton yana da cikakkiyar masaniya game da zargin shugaban na matsin lamba kan Ukraine don ganin ta gudanar da bincike kan Biden.

Tuni Kwamitin Dokoki na Majalisar Kasar ya amince da matakin gabatar da wani kudiri a gaban zauren majalisa wanda zai bayar da damar tuhumar Trump a hukumance .

Shugaban Kwamitin Dokokin, James McGovern, ya ce, akwai gagarumar hujjar da ke nuna cewa, da yiwuwar shugaba Trump ya yi karan tsaya ga kundin tsarin mulkin Amurka.

Mr. Trump dai, ya caccaki wannan binciken a kansa, yana mai alakanta shi da bita da kullin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.