Isa ga babban shafi
Bolivia

Morales ya yi hijirar siyasa zuwa Mexico

Shugaban Bolivia mai murabus, Evo Morales ya karbi tayin samun mafakar siyasa a Mexico, kwana guda da zanga-zangar ‘yan adawa ta tilasta masa sauka daga karagar mulki bayan sun zarge shi da tafka magudin zabe.

Shugaban Bolivia Evo Morales mai murabus
Shugaban Bolivia Evo Morales mai murabus HO / Bolivian Presidency / AFP
Talla

A wani sakon Twitter da ya wallafa, Morales ya ce, abin takaici ne ficewar daga Bolivia, amma nan gaba zai dawo kasar cikin kocin lafiya da karsashi. In ji shi.

Ministan Harkokin Wajen Bolivia, Marcelo Ebrard ya tabbatar cewa, tuni Mr. Morales ya shiga jirgin sama na gwamnatin Mexico.

A halin yanzu , Kwamandan sojojin Bolivia ya bai wa dakarunsa umarnin mara wa jami’an ‘yan sanda da suka yi arangama da magoya bayan Morales.

Rahotani sun ce, akalla mutane 20 sun jikkata a arangamar da aka yi.

Gabanin ficewarsa, Morales ya bukaci magoya bayansa da su yi watsi da abin da ya kira ‘bakin mulkin’ da ya tilasta masa yin murabus, yayin da mataimakiyar shugaban Majalisar Dattawan Kasar ta ce, za ta jagoranci kasar a matsayin shugabar rikon-kwarya har sai an gudanar da sabon zabe.

Tun shekarar 2006, Morales ya dare kan karagar mulkin Bolivia, yayin da a cikin watan Oktoban da ya gabata ya yi tazarce bayan an ce ya sake lashe zaben kujerar shugabncin kasar karo na hudu. Sai dai wata tawagar kwararrun jami’an tantancewa daga Amurka ta ce, an tafka mayan kura-kurai a zaben na baya-bayan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.