Isa ga babban shafi
Bolivia

Shugaban kasa ya yi murabus saboda zanga-zanga

Shugaban Bolivia, Evo Morales ya yi murabus daga kujerarsa bayan zanga-zangar makwanni uku da aka gudanar ta nuna adawa da sake zaben sa a karo na hudu, yayin da sojoji da ‘yan sandan kasar suka juya masa baya.

Shugaban Bolivia Evo Morales mai murabus
Shugaban Bolivia Evo Morales mai murabus HO / Bolivian Presidency / AFP
Talla

Dandazaon jama’a ya bige da murna a kan titunan La Paz jim kadan da sanar da murabus din Morales wanda ya kasance shugaban kasa mai ci mafi dadewa kan karaga a yankin Latin Amurka.

A yayin bikin murnar kawo karshen mulkinsa, jama’ar kasar sun yi ta yin wasan tarsatsin wuta tare da daga tutar kasar sama mai launin ja da shudi da kuma kore.

Madugun ‘yan adawar kasar wanda ya kara da Morales a zaben watan Oktoba, Carlos Mesa, ya bayana cewa, Bolivia ta koya wa duniya darasi, yana mai cewa kasar za ta zama tamkar sabuwa.

Wata tawagar kwararrun jami’an tantancewa daga Amurka ce ta gano cewa, an tafka gagrumin kuskure a zaben na watan Oktoba, lamarin da ya diga ayar tambaya kan sahihancin nasarar Morales.

Tun shekarar 2006, Morales ya dare kan karagar mulkin Bolivia, yayin da a bana ya sake neman sabon wa’adi na hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.