Isa ga babban shafi
Bolivia

Masu zanga - zanga sun kwace kafafen yada labarai a Bolivia

‘Yan adawa da ke zanga – zanga a Bolivia sun karbe kafafen yada labarai biyu malllakin gwamnatin kasar, kana suka tilasta musu katse shirye – shiryensu , yayin da wasu ‘yan sanda da ke tsaron fadar shugaba Evo Morales suka yi watsi da aikin nasu, a kasar da rikicin zaben da ake takaddama a kai ke ci gaba da ruruwa.

Shugaban Bolivia Evo Morales
Shugaban Bolivia Evo Morales REUTERS/Manuel Claure
Talla

Masu zanga – zangar sun afka wa ofisoshin tashoshin talabijin da radiyo na kasar, suka tarwatsa ma’aikata, suna mai zargin su da goyon bayan shugaba Morales,

Morales, shugaba mafi dadewa a kan karagar mulki a yankin Latin Amurka ya lashe zaben 20 ga watan Oktoba, amma jinkirin kwana guda da aka samu wajen bayyana sakamakon zaben ya janyo zargin coge.

An ga wasu m’aikata su 40 suna barin ginin dake kunshe da kafafen yada labaran biyu yayin da masu zanga – zanga da suka kai 300 suke ta kunduma musu ashar. Bayan haka ne kuma aka ji kafafen biyu suka shiga watsa kade – kade zalla.

Wannan ne tsageranci na baya – bayan nan da masu zanga – zangar suka yi tun da suka fara korafin magudi a zaben da aka bayyana shugaba Morales a matsayin wanda ya lashe.

Shugaba Evo Morales ya caccaki wannan mataki da masu zanga – zanga suka dauka, yana cewa ba su yi halin masu kare dimokaradiyya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.