Kiris ya rage mummunan al'amari ya faru a Faransa
Jami’an ‘yan sandan Faransa sun cafke wani mutum da ya afka cikin gidan adana kayayyakin tarihi a cikin tsakar daren da ya gabata, in da ya yi barazanar haddasa mummunan ala’amari.
Wallafawa ranar:
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike da zummar gano wadanda ke da hannu wajen far wa gidan tarihin da ke garin Saint-Raphael a kudancin Faransa.
Tuni jami’an tsaro da suka hada da kwararru a fannin kwance bama-bamai suka killace gidan tarihin wanda a a wani bangare na jikin bangonsa aka rubata cikin harshen Larabci cewa, « Wannan gidan zai zama tamkar jahannama »
Rahotanni sun ce, har yanzu, mutumin da aka cafke ya ki cewa uffam ga jami’an tsaro.
Jami’an ‘yan sanda ba su fayyace ko mutumin na dauke da makamai ko kuma akwai sauran ‘yan uwansa da ke labe a cikin gidan tarihin ba.
Ana sa ran hukumomi da magajin garin Saint-Raphael su gudanar da taron manema labarai wani lokaci a yau Laraba domin karin bayani kan wannan al’amari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu