Isa ga babban shafi
Duniya

Taron kasashen G20 a Japan

Ministocin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 dake gudanar da taron su a Japan sun bayyana damuwa matuka ganin ta yada ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin manyan kasashe dangane da batuttuwa da suka jibanci kasuwanci, wanda hakan zai iya ila ga tattalin arzikin Duniya.

Taron kasashen G20 a Fukuoka dake kasar Japan
Taron kasashen G20 a Fukuoka dake kasar Japan REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

A baya dai kasar Amurka ta saka haraji zuwa wasu kayaki da ake shigo da su daga China yayinda China ta dau wasu matakai a kai, hakan bai dace ba a cewar Ministan Japan Taro Aso dake Shugabantar zaman taron na Fukuoka a kudu maso yammacin kasar ta Japan.

Haka zalika Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire, ya danganta abinda dake faruwa tsakanin manyan kasashen da cewa lamari ne dake mayar da hannun agogo baya da kuma zai haifar da cikas zuwa ga batutuwan da suka shafi cinikaya a kasuwanin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.