Isa ga babban shafi
Amurka-Ghana

Amurka ta dakatar da bai wa 'yan kasar Ghana Visa

Amurka za ta fara hana ilahirin al’ummar kasar Ghana takaddar visa daga ranar 4 ga watan da mu ke ciki na Fabarairu, bayan matakin Ghana na kin amincewa da karbar daruruwan al’ummarta da ke zaune a Amurkan wadanda ta ke shirin korowa gida.

Daga ranar 4 ga watan Fabarairun shekarar nan haramcin bizar zai fara kan al'ummar Ghana a cewar Amurka har zuwa lokacin da kasar za ta samar da gyara wajen karbar tarin al'ummar da ke zaune ba bisa ka'ida ba a Amurkan
Daga ranar 4 ga watan Fabarairun shekarar nan haramcin bizar zai fara kan al'ummar Ghana a cewar Amurka har zuwa lokacin da kasar za ta samar da gyara wajen karbar tarin al'ummar da ke zaune ba bisa ka'ida ba a Amurkan iafrica.com
Talla

Matakin hana bizar ga Al’ummar Ghana a cewar Amurka ya na da nasaba da yadda ‘yan Ghanar kan yi tururuwa tare da tarewa can a sassan kasar ta America ba bisa ka’ida ba, ba tare da tunanin gida ba, inda kuma bayan Washington ta kudiri aniyar mayar da su Accra, gwamnatin Ghana ta yi biris ba tare da nuna bukatar karbarsu ba.

Wata sanarwar ma’aikatar tsaron ciki gida a Amurkan ta ruwaito, sakataren harkokin tsaron kasar Mike Pompeo na umartar Ofishin jakadancin Amurkan da ke can Accra da ya dakatar da bayar da izinin shiga Amurkan ga ‘yan kasar.

Matakin hana bizar wanda ya hadar harda jami’an diflomasiyyar Ghanan da aka tura Amurka, sanarwar ta ce zai ci gaba da fadada har zuwa lokacin da kasar za ta dauki matakan da suka kamata.

Ghanar wadda kawo yanzu ba ta ce uffan kan matakin na Amurka ba, tun a shekarar 2016 ne Amurka ke shank an ta wajen ganin ta amincewa da dawo da mutanen gida.

Sakataren Ma’aikatar tsaron ciki gida na Amurka Mr Kirstjen Nielsen ya ce yanzu haka dai akwai ‘yan Ghana fiye da dubu 7 da ke zaune a sassan Amurka ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.