Isa ga babban shafi
Venezuela-Maduro

Trump ya goyi bayan yunkurin kifar da gwamnatin Maduro

Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan matakin shugaban majalisar dokokin Venezuela, kuma jagoran ‘yan adawar kasar Juan Guaido, wanda ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa.

Yanzu haka dai ana ci gaba da zanga-zanga a sassan kasar ta Venezuele, zanga-zangar da ta kunshi masu goyon bayan shugaba Maduro da kuma masu fatan kifar da gwamnatinsa.
Yanzu haka dai ana ci gaba da zanga-zanga a sassan kasar ta Venezuele, zanga-zangar da ta kunshi masu goyon bayan shugaba Maduro da kuma masu fatan kifar da gwamnatinsa. REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Cikin sakon goyon bayan ‘yan adawar da ya aike, shugaba Trump ya bayyana gwamnatin shugaba mai ci Nicolas Maduro a matsayin haramtacciya saboda rashin sahihancin zaben da ya bashi damar waádi na biyu, zalika majalisar dokokin kasar ta Venezuela, ta dade da kada kuriár haramta shugabancinsa.

Shugaban na Amurka ya kuma bukaci, sauran kasashe su goyi bayan kawar da haramtacciyar gwamnatin Nicolas Maduro, matakin da yace Amurkan za ta amfani da dukkan karfinta na tattalin arziki da Diflomasiyya wajen tabbatar da shi.

Shelar nada kansa bisa shugabancin Venezuela da Juan Guaido ya yi, ya zo a dai dai lokacin dubban ‘yan kasar suka amsa kiransa na gudanar da gagarumar zanga-zangar neman tilastawa shugaba mai ci Nicolas Maduro yin Murabus.

Sai dai fa zanga-zangar da ke gudana a Venezuelan ta zo ne ta fuskoki biyu, domin yayin da dubban ‘yan kasar ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Maduro, wasu dubban kuwa na gudanar da ta su ce don nuna goyon bayansu ga shugaban, a dai dai lokacin da kasar ke bikin tunawa da ranar juyin juya halinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.