Isa ga babban shafi
Amurka

Trump da Kim Jong-un za su sake ganawa

An tsaida watan Fabarairu, a matsayin lokacin da za a sake ganawa karo na biyu, tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un, bayan ganawa a tsibirin Sentosa da ke Singapore. 12/6/2018.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un, bayan ganawa a tsibirin Sentosa da ke Singapore. 12/6/2018. AFP/Saul Loeb
Talla

Ko da yake ba a tsaida lokaci da wurin ganawar ba, kakakin shugaban Amurka, Sara Sanders, ta ce wani lokaci a karshen watan na Fabarairu shugabanin za su tattauna.

An cimma matsayar ce, bayan ziyarar da Kim Yong Chol, wani na hannun daman shugaban Korea ta Arewa ya kai birnin Washington a ranar Juma’a, inda ya gana tsawon mintuna 90 da wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka, kan aiwatar da yarjejeniyar, yin watsi da shirin Korea ta Arewan na mallakar makaman nukiliya.

Ganawar Kim Jong-un da Donald Trump ta farko, kan batun kawo karshen makaman nukiliya a yankin Korea, ta gudana ne a kasar Singapore, cikin watan Yuni na shekarar bara.

A wannan karon dai kasar Vietnam ta yi tayin karbar bakuncin ganawar, sai dai Amurka da Korea ta Arewan ba su ce komai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.