Isa ga babban shafi
Amurka-Korea

Zan sauya matsaya kan makamin nukiliya- Kim

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya ce, ya dukufa kan shirin kawo karshen mallakar makamin nukiliya amma ya gargadi cewa, zai sauya matsaya muddin Amurka ta ci gaba da kakaba musu takunkumai.

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa a yayin gabatar da jawabin shiga sabuwar shekara a ranar Talata
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa a yayin gabatar da jawabin shiga sabuwar shekara a ranar Talata KCNA/via REUTERS
Talla

Shugaban ya furta haka ne a yayin gabatar da jawabin shiga sabuawar shekara ga al’ummar kasar a ranar Talata, in da ya ce, matukar Amurka ba ta cika alkawuranta ba, to babu wani zabi da ya rage musu illa lalubo wata sabuwar hanyar kare ‘yancin kasar.

A cikin watan Yunin da ya gabata ne a Singapore, Mr. Kim ya gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump kan batun kwance makamin na nukiliyar, amma har yanzu babu wani gagarumin sakamakon da ya biyo bayan wannan ganawa da ta farfado da alakar diflomasiya a tsakaninsu.

Shugabannin biyu sun ganawa ne bayan Koriya ta Arewa ta gudanar da jerin gwaje-gwajen makamai masu linzami, ciki har da wanda ta ce, zai iya riskar tsakiyar Amurka, abin da ya zafafa musayar yawu tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Kim ya bayyana cewa, a shirye yake ya sake wata ganawa da Trump a ko wani lokaci daga yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.