Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Taliban ta bukaci janye dakarun kasashen ketare daga Afghanistan

Kungiyar Taliban ta sanar da wata ganawa tsakaninta da wakilan Amurka da na Pakistan a wani mataki da ke yunkurin sasanta rikicin Afghanistan da aka kwashe shekaru ana fafatawa ba tare da samun galaba ba.

Taliban ta yi ikirarin bin matakan da suka dace wajen kawo karshen rikicin kasar ta Afghanistan matukar basu ci karo da dokokinta ba.
Taliban ta yi ikirarin bin matakan da suka dace wajen kawo karshen rikicin kasar ta Afghanistan matukar basu ci karo da dokokinta ba. Reuters
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta nuna cewar Shugabannin Taliban sun gana da Jakadan Amurka, Zalmay Khalilzad a jiya litinin, kuma ana fatar cigaba da tattaunawar a nan gaba.

Kungiyar ta ce tayi kuma tattaunawa mai tsawo da wakilan kasashen Saudi Arabia da Pakistan da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda suka bayyana bukatar su kan janye dakarun kasashen waje daga Afghanistan.

Amurka ta sanar da cewar, ana tattaunawa a Daular Larabawa domin samo hanyar magance rikicin kasar ta Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.